Gwamna Sanwo-Olu Ya Bukaci Shugabannin Afrika Su Hade Kai Don Yakar Safarar Mutane Da Kisan Gilla

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya kira shugabannin ƙasashen Afrika da su haɗa kai wajen yaƙi da safarar mutane da kisan gilla na neman arziki, domin kare rayuka, hukunta masu laifi, da dawo da mutuncin waɗanda abin ya shafa.

Sanwo-Olu, wanda Sakatariyar Gwamnatin Jihar Legas, Hajiya Abimbola Salu-Hundeyin, ta wakilta, ya yi wannan kira ne a taron farko na Africa Colloquium Against Human Trafficking, wanda aka gudanar a Legas ranar Alhamis.

Gwamnan ya bayyana cewa, irin waɗannan miyagun laifuka suna ƙasƙantar da mutunci da ‘yancin ɗan Adam, musamman mata da ƙananan yara da ke fuskantar wahalhalu, bautar dole, da cin zarafi ta jiki da ta sihiri.

Ya ce:

Safarar mutane ba matsala ce ta nesa ba  tana faruwa a nan kuma tana shafar kowa. Dole ne mu tashi tsaye tare wajen yaƙar wannan bala’i ta hanyar haɗin kai, bayanan sirri, da tausayi.”

Ya ƙara da cewa gwamnatoci dole ne su haɗa kai da ƙungiyoyin farar hula, shugabannin addinai da na gargajiya, da kuma ‘yan kasuwa domin fallasa masu aikata laifin da kuma kare wadanda abin ya rutsa da su.

Sanwo-Olu ya kuma bukaci a kara tsaurara doka domin tabbatar da cewa wadanda aka kama suna fuskantar hukunci cikin gaggawa, yayin da wadanda aka zalunta suke samun kulawa da gyara rayuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Legas ta kafa Kwamiti na Musamman Kan Yakki da Safarar Mutane, tare da hadin gwiwa da Hukumar NAPTIP da kungiyoyin kasa da kasa, domin kara karfi wajen gurfanar da masu laifi, wayar da kai, da taimakon wadanda suka tsira daga wannan bala’i.

“A nan Legas, muna aiki tare da abokan hulda domin karfafa tsarin shari’a da kuma ba wa wadanda abin ya shafa damar sake gina rayuwarsu. Amma gwamnati kadai ba za ta iya cin nasara ba – dole ne a hada kai da hukumomin shari’a, jami’an tsaro, shugabannin al’umma, da kungiyoyin addinai,” in ji shi.

A nasa jawabin, Babban Alƙalin Jihar Legas, Mai Shari’a Kazeem Alogba, ya buƙaci ƙarin kulawa daga al’umma, inganta aiwatar da doka, da hadin gwiwar kasa da kasa don kawar da wannan barna.

Ya ce, ko da yake an daina bautar mutane shekaru aru-aru da suka wuce, to amma sifofinta na zamani irin su safarar mutane, kisan gilla, da safarar sassan jiki  na ci gaba da faruwa saboda dalilan kuɗi.

“Ba za mu iya magance matsalar ba sai mun fuskanci wasu al’adunmu da ke bai wa irin wadannan laifuka hujja. Amfani da ɗan Adam don wani tsafi ko wata buƙata, ko da an yi masa ado da al’ada, mugunta ce. Yaƙi dole ne ya fara daga cikin al’umma,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Prince Lateef Fagbemi (SAN), ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da yaƙi da safarar mutane, kisan gilla, da safarar ‘yan gudun hijira a faɗin nahiyar Afrika.

Wakiliyar sa a wajen taron, Mrs Ezinne Nwaokoro, wacce ke jagorantar shirin Trafficking in Persons and Smuggling of Migrants (TIPSOM) a ma’aikatar shari’a, ta ce gwamnati na aiki don rushe hanyoyin da masu safarar mutane ke bi ta hanyar haɗin kai na doka, diflomasiyya, da matakan al’umma.

Ta ƙara da cewa Babban Lauyan ƙasa ya sanya gyaran doka da ƙarfafa hulɗar NAPTIP da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa cikin ajandar sauye-sauyen yaƙi da safarar mutane.

Post a Comment

Previous Post Next Post