Wani abu da masana tsaro ke nuna damuwa a kai shi ne yadda ƙungiyar ke amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare, kamar amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai ko kuma wajen tattara bayanai.
Kuma wataƙila sabunta fasahar kungiyar ne ya sa hare-haren nata suka yawaita saɓanin a baya lokacin da a koyaushe sai dai su kai samame.
Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce ko a watan Disamban 2024, mayaƙan sun kai wa sojoji hare-hare har sau hudu ta hanyar sanya bama-bamai jikin jiragen marasa matuƙi.
Dakta Kabir ya bayyana cewa ba yanzu waɗannan ƙungiyoyi suka fara amfani da jirgi maras matuƙi ba.
"A 2019 mun ga lokuta inda waɗannan ƙungiyoyi suke amfani da jirage maras matuƙa amma kawai domin leƙen asiri, suna dasa bama-bamai a waɗannan jirage."
Alƙaluman wata ƙungiyar "ACLED" mai sanya ido kan tsaro da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a wannan shekarar ta 2025.
To sai dai kuma kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce bisa alƙaluman da ya tattara, ƙungiyar Boko Haram ta kai hare-hare har sau 199 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Satumbar 2025.
Shugaban kamfanin Dakta Kabiru Adamu ya ce da dama masu nazarin ayyukan Boko Haram ba sa banbance tsakanin ƙungiyar da sauran ƙungiyoyi masu riƙe da makamai.
"Wani abu mai muhimmanci da masu bincike ba sa banbantawa shi ne akwai ƙungiyoyin da ba na Boko Haram ba da ke kai hari sai a kira su da Boko Haram. Misali akwai ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai amma ba sa iƙrarin jihadi, idan suka kai hari sai a yi kuɗin goro a ce Boko Haram," in ji Kabiru Adamu, Beacon Security and Intelligence Limited.
