Kungiyar SAF Da Gwamnatin Sokoto Sun Hada Kai Da Jami’an Tsaro Don Ceto Daliban Tsangaya Daga Barace-Barace

  Gwamnatin Jihar Sokoto tare da haɗin gwiwar Kungiyar Sokoto Advocacy Foundation (SAF) sun gudanar da wani muhimmin taro da jami’an tsaro domin tattauna matakan da ake ɗauka na ceto daliban Tsangaya (Almajirai) daga barace-barace a tituna.

Almajirai

Taron, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Sokoto, ya haɗa wakilai daga ‘yan sanda, hukumar NSCDC, da kuma masu rike da sarautun gargajiya, inda dukkan su suka nuna goyon bayansu ga wannan shiri.

Ofishin Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Sokoto ya bayyana cewa, wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na gyara tsarin karatun Almajirai, domin tabbatar da cewa yara masu karatun addini a Tsangaya suna samun ilimin addini da na zamani cikin yanayi mai tsabta da mutunci.

Jami’an sun kuma jaddada cewa barace-barace na kan hanya na jefa yara cikin haɗari, cin zarafi da kuma rashin kulawa, don haka akwai buƙatar haɗin kai tsakanin hukumomi da al’umma wajen kare haƙƙoƙin su da tabbatar da kyakkyawar makoma gare su.

Post a Comment

Previous Post Next Post