Alƙalai a Kamaru sun yi watsi da buƙatar da aka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaɓen shugaban ƙasar ko kuma su soke zaɓen baki ɗaya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin.
Zanga-zanga ta ɓarke a wasu manyan biranen ƙasar, inda ƴan adawa suka yi zargin an tafka kura-kure a zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba.
Alƙalan kotun tsarin mulki sun yi watsi da ƙorafi har takwas da aka gabatar masu, domin a cewar su babu cikakkiyar shaida mai tabbatar da su.
Ɗan takarar ƴan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wani iƙirari da ke nuna cewa ya zarce shugaba Paul Biya mai shekara 92 a duniya, wanda kuma ke neman wa'adin mulki na bakwai.
Tchiroma Bakary mai shekara 76 da haihuwa, tsohon kakakin gwamnatin Biya ne, wanda a yanzu yake neman ƙwace mulki a hannunsa.
Ya ƙi yarda ya tura nasa ƙorafi zuwa kotun kundin tsarin mulkin ƙasa, kuma ya zaɓi ayyana kansa a matsayin ''Halartacce shugaban ƙasa.
A wani saƙon shafukan sada zumunta da ya fitar, Tchiroma Bakary ya ce ya lashe zaɓen bayan samun kashi 55 cikin ɗari na jimillar ƙuri'un da aka kaɗa.
Ya ce ''Idan har majalisar kundin tsarin mulki ta gaza hukunta maguɗi ta kuma zaɓi goyon bayan maguɗi, to babu shakka ta kauce hanya''. Tchiroma Bakary ya kuma yi gargaɗin cewa ''jama'a za su juya masu baya da kuma yi masu barazana.
Jam'iyyar shugaba Biya ma ta yi watsi da iƙirarin Tchiroma Bakary na samun nasara a zaɓen tana mai cewa majalisar kunɗin mulki ce kaɗai ke da ikon sanar da sakamako.
Zaman jiran sakamakon da ake ciki a Kamaru ya jefa tsoro da fargaba a zukatan jama'a. Haka Kuma, cocin katolika ma ta shiga maganar a farkon makon nan, inda ta buƙaci alƙalan kotu su tabbata sun yi adalci.
