Matashin Dan Najeriya Mai Shekaru 18 Ya Shiga Tarihi Bayan Ya Samu Lasisin Tuki Jirgin Sama S Amurka

Wani matashin ɗan Najeriya, Mohammed Aminu Sani, ya shiga cikin tarihi bayan ya zama ɗaya daga cikin matasan Najeriya mafi ƙuruciya da suka samu lasisin tukin jirgin sama na kasuwa (Commercial Multi-Engine Pilot License) daga Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) — yana da shekaru 18 kacal.

Sani ya kammala horonsa na tukin jirgin sama a Phoenix East Aviation (PEA) da ke Daytona Beach, Florida, cikin watanni goma kacal, abin da ake ɗauka a matsayin babbar nasara a fannin jiragen sama. Abin ban sha’awa, bai taɓa faduwa ba a kowane mataki na jarabawar horonsa — abin da ke nuna ƙwarewa, tsari, da jajircewa.

“Tashin jirgin sama burina ne tun ina ƙarami, yau kuma ina alfahari da cewa na cika wannan buri,” in ji Sani. “Wannan tafiya cike take da aiki tukuru, ladabi da ƙwazo. Ina fatan labarina zai zaburar da sauran matasa su bi burinsu ba tare da gajiya ba.”

An haifi Sani kuma aka raina shi a Abuja, inda ya gina tubalin iliminsa. Ya sami takardar kammala sakandare (High School Diploma) daga Al-Hidaayah Academy, sannan ya yi karatun Economics Foundation a The Regent College, Abuja, inda ya fito da kyakkyawan sakamako (Distinction).

Gwanintarsa da sha’awarsa ta tashi jirgi ne suka buɗe masa ƙofa zuwa Phoenix East Aviation, ɗaya daga cikin makarantu mafi ƙima a duniya wajen horar da masu tuƙa jiragen kasuwanci daga ƙasashe sama da 70.

A lokacin horonsa, Sani ya yi tashin dare, jirage na tazarar ƙetare ƙasa (cross-country da kayan aiki (instrument navigation) a ƙarƙashin yanayi mai wahala. Lokacin da ya kammala, ya tara lokutan tashi da yawa a cikin jiragen multi-engine, ciki har da PA-34-200 Seneca, tare da sama da awanni 30 na jirgin nesa, wanda ya kammala da samun lasisin FAA Commercial Pilot  AMEL).

Nasarar Sani ta zo ne a lokacin da matasa da dama ‘yan Najeriya ke ƙoƙarin samun gagarumar ƙima a duniya ta hanyar ilimi da ƙwarewa. Masana harkar jiragen sama sun bayyana cewa labarinsa misali ne na abin da zai iya faruwa idan buri da dama suka haɗu.

“Tafiyar Mohammed tana nuna ƙarfin matasan Najeriya  yadda suke iya yin babban buri su kuma fafata a matakin duniya,” in ji wani malamin jirgi a Phoenix East Aviation. “Kammala irin wannan shirin ba tare da gazawa ba ko da sau ɗaya, babban abin koyi ne da ke nuna girman tunani da ƙwarewa.”

Yanzu da ya samu lasisin tuƙin jirgin kasuwanci, matashin ɗan Najeriya ɗan shekara 18 yana shirin ci gaba da neman ƙwarewa a fagen jiragen sama na duniya.

“Burina bai tsaya nan ba,” in ji shi. “Wannan ne farkon tafiyata. Ina son ci gaba da tashi sama, in koyi daga ƙwararru, kuma in sanya Najeriya ta yi alfahari a duniyar jiragen sama.”

Post a Comment

Previous Post Next Post