Magoya Bayan Mbeumo Da Ke Kamaru Sun Shawarcesa

A wasan cike gurbi na gasar cin kofin duniya (World cup Qualifier) da aka gabatar a jiya tsakanin ƙasar Mauritius da Cameroon, magoya bayan Mbeumo ɗan ƙwallon gefe na Kamaru wanda yake taka leda a ƙungiyar Manchester United, sun shawarce shi da ya tattauna da mai horas da ƙungiyar ta Manchester United Ruben Amorima kan salon zubin 'yan wasansa na 3-5-3, inda suka shawarce shi da ya koma buga 4-3-3 kamar yadda Kamaru suka buga a jiya.
Wannan shawarar ta biyo bayan irin namijinƙoƙarin da Mbeumo ɗin ya yi a wasan. Duk da ya shigo ne a mintuna na 75, amma duk da haka sai da ya zura masu ƙwallo a mintunan ƙarshe.

Post a Comment

Previous Post Next Post