Mutanen Gaza Sun Cika Tituna Da Fatan Karshen Yakin Isra’ila

 Fararen Hula Sun Nuna Ƙwazo Da Fatan Sabuwar Rayuwa Bayan Shekaru Ana Rikici.

Dubban mazauna yankin Gaza sun fito kan tituna cikin farin ciki da bege bayan jin labarin cewa Isra’ila da Hamas na tattaunawa kan tsagaita wuta. Wasu daga cikin mazauna sun bayyana cewa wannan na iya zama farkon ƙarshen yaƙin da ya hallaka dubban mutane da lalata gidaje da cibiyoyi.

Mutane sun rika yin addu’o’i da rawar farin ciki yayin da suka ce sun gaji da tashe-tashen hankula da rashin tsaro. Duk da haka, wasu sun nuna damuwa cewa za a iya samun jinkiri ko karya alkawarin tsagaita wutar, kasancewar irin waɗannan yarjejeniyoyi na baya-bayan nan sau da dama ba su daɗe ba.

Masu lura da al’amura sun ce wannan martani daga jama’a na nuna yadda mutane ke matuƙar fatan samun zaman lafiya da sake farfaɗo da rayuwa. Duk da fatan alheri, ana ci gaba da jiran tabbacin hukuma daga ɓangarorin biyu kafin a tabbatar da cikakken dakatar da yaƙin.

Post a Comment

Previous Post Next Post