‘Yan sanda sun ce bincike yana ci gaba domin kamo sauran waɗanda suka tsere.
Rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama mutune 12 da ake zargi da hannu a harin da ya yi sanadin mutuwar Somtochukwu Maduagwu, mai gabatar da shirye-shirye a tashar talabijin ta Arise , da kuma mai gadin da yake tsare ginin Unique Apartments a Katampe, Abuja.
An ce kimanin mutane 15 dauke da makamai ne suka kutsa ginin a ranar 29 ga Satumba, inda suka harbi mai gadin, Barnabas Danlami, sannan Somtochukwu ta mutu bayan ta faɗi daga bene na uku yayin ƙoƙarin tserewa.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin bayan an bi diddigin wayoyin da aka sace daga wurin, kuma daya daga cikinsu, Shamsudeen Hassan, ya amsa cewa shi ne ya harbi mai gadin lokacin harin.