Majalisar Tarayya Na Son Samar Da Doka Don Kula Da Harkar Kudin Kirifto a Najeriya

 

Crypto

‘Yan majalisa sun fara shirin duba yadda za a sanya dokoki don lura da kasuwancin kuɗin intanet (cryptocurrency) a Najeriya domin hana zamba da kare tattalin arzikin ƙasa.

Majalisar Tarayya ta bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da tsarin doka da zai bai wa gwamnati damar sa ido kan harkokin kuɗin kirifto (crypto), ganin yadda harkar ke ƙaruwa cikin matasa da ‘yan kasuwa a Najeriya.

An bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen hana amfani da kuɗin crypto wajen aikata laifuka kamar safarar kuɗi da zamba ta intanet. Majalisar ta kuma ce za ta tattauna da masana harkar kuɗi da hukumomin tsaro domin tsara doka mai inganci wacce za ta dace da tsarin Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post