INEC: Mahmood Yakubu ya mika wa May Agbamuche-Mbu Ragamar Shugabanci A Matsayin Mai Rikon Kwarya

Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya kammala wa’adinsa a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Mrs. May Agbamuche-Mbu, wadda za ta jagoranci hukumar a matsayin mai rikon kwarya.

Bikin miƙa mulkin ya gudana ne a ranar Talata yayin wani taro da ake yi tare da Kwamishinonin Zabe na Jihohi (RECs) a hedkwatar INEC da ke Abuja.

Agbamuche-Mbu, wadda ita ce mafi tsawon shekaru a matsayin kwamishiniya a hukumar, za ta ci gaba da jagorantar harkokin hukumar har sai an nada sabon shugaban dindindin.

Yayin da yake sanar da sauyin shugabanci, Farfesa Yakubu ya roƙi ma’aikatan hukumar da su ba wa sabuwar shugabar cikakken goyon baya da haɗin kai.

“A yau na miƙa ragamar hukumar ga Mrs. May Agbamuche-Mbu a matsayin Shugabar Riƙo ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa. Ina roƙon duk kwamishinoni da daraktoci su nuna mata irin goyon bayan da kuka ba ni,” in ji shi.

Wannan ci gaban ya nuna canjin wucin gadi a jagorancin hukumar yayin da ake ci gaba da shirye-shirye na gudanar da ayyukan zaɓe a fadin ƙasar.

Mrs. Agbamuche-Mbu, wadda ƙwararriya ce a fannin lauya da gudanarwa, ta kasance ɓangare na ƙungiyar shugabannin INEC tun bayan da aka naɗa ta a matsayin Kwamishiniyar Ƙasa, kuma ana sa ran za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren sauye-sauyen da hukumar ke yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post