Malaman lafiya suna ta famar bincike don tabbatar da lafiyar al'umma. Bacci wani abu ne da ke taimaka wa gangar jiki, haka kuma yana taimaka wa ƙwaƙwalwa wajen samun nutsuwa sosai a yayin da mutum ya samu damar yin sa. Ga wasu shawarwari da likitoci suka bayar ta yadda ɗan'Adam zai kyautata baccinsa.
1.Ka rage cin abinci kafin kwanciya
Cin abinci kusa da lokacin bacci na iya kawo acid reflux (ulcer pain) da Matsalolin ciki. Ka dakata da cin abinci aƙalla awa biyu kafin ka kwanta domin hanji ya yi aiki cikin sauƙi
2. Ka sha ruwa kaɗan kafin bacci
Kar ka sha ruwa da yawa har ya hana ka yin bacci saboda fitsari. Idan za ka sha ruwa, ka sha kaɗan.
3. Ka yi addu’a da karatun Al-Qur’ani kafin bacci
Yin addu'a da karatun Al'Qur'ani yana rage damuwa, yana daidaita bugun zuciya, kuma yana kawo nutsuwa ta zahiri da ta ruhi.
4. Ka tabbatar ɗakinka yana da tsabta da iska mai kyau tana shigowa
Bacci a ɗaki mai tsafta, sanyi, da ƙamshi na taimaka wa ƙwaƙwalwa ta huta sosai. Pillow da zanin gado su kasance masu tsafta domin guje wa cututtuka da allergies.
5. Ka guji shan kofi ko shayi kafin bacci
Caffeine yana hana ƙwaƙwalwa samun natsuwa da dare, yana jinkirta lokacin bacci, musamman idan an sha bayan ƙarfe shidda na yamma.
6. Ka kashe haske gaba ɗaya
Haske (ko daga fitila ko waya) na iya hana ƙwaƙwalwa shiga “deep sleep mode”.
Mutane da yawa ba sa kiyaye baccinsu, wanda hakan ba ƙaramar illa yake haifarwa ga lafiyarsu ba.

Don haka, bayan karanta wannan binciken mai ƙumshe da shawarwari, yana da kyau a kula da wajen kwanciya domin ƙwaƙwalwa ta samu damar shiga bacci mai nauyi (Deep Sleep Mode)