Supermoon Na Farko Tun Nuwamba 2024 Zai Bayyana A Watan Oktoba

 Cikakken watan Oktoba zai bayyana da girma da haske fiye da yadda aka saba, yayin da yake kusa da doron ƙasa, abin da bai sake faruwa ba tun ƙarshen shekarar 2024.

Supermoon

A cewar masana sararin samaniya, wannan supermoon ɗin ana sa ran zai bayyana tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga Oktoba, inda zai yi haske sosai saboda kusancinsa da doron ƙasa fiye da yadda yake a lokutan da sauran watanni ke cikawa.

Supermoon yana faruwa ne idan cikakken wata ya zo daidai da lokacin da yake kusa da ƙasa (wanda ake kira perigee), hakan yana sa ya zama mafi girma da kusan kashi 14% da kuma haske da kusan kashi 30% fiye da yadda aka saba gani.

Masana sun ce ba sai an yi amfani da kayan hangen taurari ba domin ganin wannan abin al’ajabi; a buɗe idanu, da sarari mai kyau, kowa zai iya ganin kyakkyawan hasken cikakken watan daga ko’ina.

Ana sa ran wannan zai zama na farko daga cikin uku a shekara ta 2025 - inda sauran supermoon za su sake bayyana a Nuwamba da Disamba.

Post a Comment

Previous Post Next Post