‘Yan Najeriya Uku Sun Samu Manyan Mukamai A Hukumar FIFA

Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Musa Gusau; lauya mai ƙwarewa, Abdulhakeem Mustapha (SAN); da kuma gogaggen ‘yar jarida wacce kuma mamba ce a kwamitin gudanarwa na NFF, Aisha Falode, sun samu naɗe-naɗe a muhimman kwamitocin dindindin na FIFA.

GusauWannan ci gaban mai tarihi ya ƙara tabbatar da tasirin Najeriya a harkokin gudanar da ƙwallon ƙafa na duniya, inda aka sanya ƙwarewar ‘yan Najeriya cikin tsakiya na tsarin yanke shawara na FIFA.

Shugaban NFF, Gusau, ya shiga cikin Kwamitin Gasar Ƙwallon Ƙafa ta Maza ta Ƙungiyoyi (FIFA Men’s Club Competitions Committee), yayin da Abdulhakeem Mustapha (SAN) da Aisha Falode suka samu naɗin zama mambobi a Kwamitin Yaƙi da Nuna Bambanci da Wariyar Launin Fata (FIFA Anti-Racism & Anti-Discrimination Committee) da kuma Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗar Jama’a (Media & Communications Committee), bi da big.

Naɗin nasu ya zo ne kwanaki kaɗan bayan tsohon shugaban NFF, Amaju Melvin Pinnick, ya samu mukamin mataimakin shugaban kwamitin FIFA na gasar ƙungiyoyin ƙasashe ta maza (FIFA Men’s National Teams Competitions Committee) — wanda ke da rawar gani wajen tsara da gudanar da dukkan wasannin ƙungiyoyin ƙasashe na maza a duniya.

Pinnick ya bayyana farin cikinsa kan naɗin, yana mai cewa wannan wata alama ce ta muhimmancin Najeriya da hazakar ‘yan ƙasarta a fagen ƙwallon ƙafa ta duniya.

Ya ce:

“Ina matuƙar jin daɗin ci gaba da hidima a FIFA kuma ina alfahari da yin aiki tare da Robert Harrison, shugaban kwamitin gasar ƙungiyoyin ƙasashe ta maza.
Ina taya Shugaba Gusau, Abdulhakeem Mustapha, SAN, da Aisha Falode murna bisa wannan naɗi mai daraja. Tare, za mu wakilci sabon zamani na ƙwarewa, gaskiya, da ƙirƙira ga ƙwallon ƙafa ta Najeriya a matakin duniya.”

Post a Comment

Previous Post Next Post