An haifi David Ben-Gurion a ranar 16 ga watan Oktoba 1886 a birnin Płońsk na ƙasar Poland a daular Rasha (kasar Poland ta yau).
David Ben-Gurion shi ne wanda ya kafa kuma ya zama firimiya na farko na kasar Isra'ila, fitaccen shugaban Sahayoniyawa, kuma jigo a kafuwar Isra'ila, asalinsa baƙo ne haifaffen ƙasar Poland wanda yayi hijira zuwa Falasdinu kuma ya yi aiki a matsayin Firayim Minista na Isra'ila daga 1948-1953 da kuma daga 1955-1963.
Ben-Gurion ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙirar ƙasar Isra'ila. A matsayinsa na shugaban kwamitin zartarwa na Hukumar Yahudawa daga 1935, ya shirya yadda al'ummar Yahudawa a Falasɗinu za su sami ƙasa ta kansu. A ranar 14 ga Mayu, 1948, ya yi shelar kafa ƙasar Isra'ila kuma ya sanya hannu kan sanarwar 'yancin kai na Isra'ila. A lokacin yaƙin Larabawa da Isra'ila a shekara ta 1948, ya jagoranci ƙasar, inda ya haɗa rudunonin mayaƙan Yahudawa daban-daban cikin rundunar tsaron Isra'ila (IDF) da kuma kula da dabarun soji.
A matsayinsa na firayim minista, Ben-Gurion ya kafa cibiyoyi da ababen more rayuwa a Isra'ila. Ya kula da kwararar baƙin haure yahudawa. Ya kuma ba da umarnin mamaye yankin Sinai na Masar a shekarar 1956 a lokacin rikicin Suez.
.Ritaya
Ben-Gurion ya yi ritaya a shekara ta 1963 in da ta koma kibbutz na Sde Boker a cikin hamadar Negev. Bayan ya fice daga jam’iyyarsa a shekarar 1965 saboda taƙaddamar siyasa, ya yi ritaya daga siyasa a shekarar 1970, kuma ya mayar da hankali wajen rubuta littafin tarihinsa. Ya rasu a ranar 1 ga Disamba, 1973, kuma an binne shi a Sde Boker.