Mutane Biyu Sun Rasu A Harin Da Aka Kai Coci Na Yahudawa A Manchester, UK

 Yan Sanda Sun Ce Ana Zargin Har Mai Kai Harin Ma Ya Rasu.

synagogue

Manchester, Birtaniya, Rahotanni daga hukumar ‘yan sanda sun tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu a wani hari da aka kai wani majami’ar Yahudawa (synagogue) a birnin Manchester, ƙasar Birtaniya.

An ce harin ya auku ne da safiyar yau, kuma ana kyautata zaton wanda ake zargin da kai harin ma ya mutu a yayin arangama.

Hukumomin tsaro sun ce sun ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da tsaron jama’a da kuma dakile duk wata barazana ta gaba. An kuma bukaci al’ummar birnin da su kwantar da hankalinsu tare da baiwa jami’an tsaro haɗin kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post