‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Mai Shekaru 62 Bisa Tilasta Karɓar Haraji Na Haramun A Madadin IPOB/ESN A Anambra

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Anambra ta kama wani mutum mai shekaru 62, mai suna Bernard Odinchefu, bisa zargin tilasta karɓar kuɗaɗen shiga na haramun a madadin ƙungiyar da aka haramta, wato Indigenous People of Biafra (IPOB), da kuma rundunar tsaronta, Eastern Security Network (ESN).

ƴansandaHukumomin ‘yan sanda sun ce an kama shi ne yayin wani samamen da rundunar ta gudanar a maɓoyar masu laifi domin rusa ayyukan IPOB/ESN da ke tsoratarwa tare da tilasta wa jama’a biyan kuɗi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa rundunar Rapid Response Squad (RRS) ta cafke Odinchefu a kauyen Isseke, ƙaramar hukumar Ihiala, inda ake zargin yana tilasta jama’a biyan haraji na haramun.

A cewar Ikenga, ana zargin wanda ake tuhumar yana karɓar kuɗi na aƙalla Naira 10,000 daga kowanne ɗan kasuwa a Orsumuoghu duk wata, tare da tilasta iyalan da ke shirya jana’iza ko wasu taruka su biya aƙalla Naira 100,000 kafin gudanar da bukukuwan.

“Binciken farko ya nuna cewa ana tura waɗannan kuɗaɗen zuwa ga kwamandansa da ke wani sansanin ta’addanci,” in ji Ikenga.

Ya ƙara da cewa an kama Odinchefu ne a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, kuma yana hannun ‘yan sanda yanzu domin ci gaba da bincike.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ikioye Orutugu, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da rusa duk wata gurɓataccen tsari da ke da alaƙa da ƙungiyoyin tayar da zaune tsaye.

“Ya jaddada cewa wannan kama wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi don kawar da dukkan waɗanda ke cin moriyar zaluntar jama’a da sunan neman ‘yancin kai,”

Post a Comment

Previous Post Next Post