Hukumar Gaskiya Ta Bayyana Cewa An Samu Yaudara da Taka Haƙƙin Ɗan Adam Tsawon Shekaru.
Seoul, Koriya ta Kudu, Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu, Lee Jae-myung, ya nemi afuwa a hukumance bisa laifuffukan da aka aikata a tsarin ɗaukar yara zuwa ƙasashen waje da aka gudanar tsawon shekaru, wanda ya ƙunshi yaudara da cin zarafi a kan yara da iyayensu.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa, shugaban ya ce: “Ina miƙa gaskiyar tausayawa da addu’ar samun sauƙi ga waɗanda aka ɗauka zuwa ƙasashen waje, iyayensu na haihuwa, da iyayen da suka karɓe su, bisa laifuffukan da suka haifar musu da wahala da baƙin ciki.”
Shugaban ya bayyana cewa gwamnati za ta ɗauki matakan kare haƙƙin yara da kuma taimaka wajen haɗa su da iyayen su na haihuwa idan hakan ya yiwu. Haka kuma, Koriya ta Kudu ta rattaba hannu kan Hague Adoption Convention a watan Yuli, domin ƙara tabbatar da tsari mai gaskiya da kariya ga yara.
An ƙiyasta cewa daga bayan Yaƙin Koriya zuwa shekarar 1999, an ɗauki tsakanin 30,000 zuwa 140,000 yara daga Koriya ta Kudu zuwa ƙasashen waje. Hukumar ta tabbatar cewa yawanci an gudanar da ɗaukewar ta hanyar ƙarya da yaudara da nufin rage nauyin kula da marasa galihu a cikin ƙasar.