Babu Wani Annabi da Aka Aiko da Izala, Tijjaniya, Kadiriyya Ko Shi'a

 Ga Jawabin Jarumi Abdullah Amdaz Game da Lamarin:

"Duka waɗannan ƙungiyoyin addinin kamar zala, ɗariƙar tijjaniyya, ƙadiriyya , Shi’a, da ma wasu ba wannan ba, mutane ne suka ƙirƙira su, babu ɗaya da aka aiko wani Annabi da ita, har tawagar Maisissika..

Abdullah Amdaz

Ku ne dai mutane kuka zaɓawa kanku su a matsayin hanyoyin addini da rayuwa, don na ce ba zanbi ɗaya daga cikinsu ba, ta yiwu akwai wata hujja ta ilimi da nake da ita. Haka don na ce zan yi, ta yiwu ina da wata hujja.

To amma fa biyayya ga Annabi Muhammad ﷺ dole ce ƙanwar na ƙi, ko ka yi ka samu tsira, ko ka ƙi ka halaka, don haka alqur’ani da Sunnah sune hanyar tsira.

Dukkan wata ƙungiya da aka kafa matuƙar ba za ta kira ka kan Kitabuwassunah ba, ba za ta tsayar da kai kan bautar Allah ɗaya ba, ka yarda aka ɗora ka a kan Igiyar zato da labarin mafarki, ka saki na Allah ka kama na wani ina tausaya maka.

Kome ka bi akwai inda ya karkata ba daidai ba, amma a bin Manzon Allah ﷺ babu komai sai saduwa da Allah lafiya!"

Post a Comment

Previous Post Next Post