NARD Ta Hana Yin Aikin Kiran Gaggawa Fiye Da Awanni 24, Ta Ce Barazana Ce Ga Rayuwar Likitoci

Ƙungiyar Likitocin gida na Najeriya (NARD) ta bayar da umarni ga mambobinta a faɗin ƙasa da su daina yin aikin kiran gaggawa na ci gaba fiye da awanni 24, tana mai bayyana al’adar a matsayin “mai kashe matasa likitoci a asirce.”

doctorWanunan umarni na NARD na ƙunshe ne a cikin sanarwar ƙarshe da aka fitar bayan Taron Ƙoli (AGM) na ƙungiyar, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Oktoba, 2025. Sanarwar ta samu sa hannun Sakatare Janar na ƙungiyar, Dr. Mohammad Suleiman; Mataimakin Sakatare Janar, Dr. Shuaibu Ibrahim; da kuma Sakataren Yaɗa Labarai da hulɗa da Jama’a, Dr. Abdulmajeed Yahya. 

Sabon tsarin ya tanadi cewa dole ne kowanne likita ya sami hutun kiran gaggawa bayan kammala wani kiran. Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin “ba wai kawai wajibi ba ne, amma muhimmanci ne,” bisa ƙa’idar kare kai da aka shimfiɗa a cikin Rantsuwar Hippocrates.

NARD ta nuna damuwa kan ƙara tabarbarewar tsarin rabo tsakanin likita da marasa lafiya a Najeriya, inda yanzu yake a kan likita ɗaya zuwa marasa lafiya 9,083, saɓanin shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadda ta ƙayyade likita ɗaya ga marasa lafiya 600. Tare da yawan jama’a sama da miliyan 240 da kuma likitocin gida kusan 11,000 kaɗai, ƙungiyar ta bayyana cewa likitocin Najeriya suna aiki kimanin awanni 106.5 a kowane mako, yayin da likitocin tiyata ke aiki har zuwa awanni 122.7 a mako.

“Wannan na nufin yin kiran gaggawa na awanni 24 sau huɗu zuwa sau biyar a cikin mako. Wannan yana jawo gajiya matuƙa, yana ƙara yawan kuskuren likitanci, yana jefa lafiyar marasa lafiya cikin haɗari, tare da yin mummunar illa ga lafiyar ƙwaƙwalwa, jiki da tunanin likitoci,” in ji sanarwar.

Likitocin sun yi kuka kan yadda abokan aikinsu da dama suka rasu a ƙarƙashin waɗannan mummunan yanayi, suna barin danginsu ba tare da tallafi ba. Sun ce: “Yayin da ƙasa ke murna, mu kuma muna binne abokanmu a shiru, ƙasar tana kallo kawai. Tambayar ita ce: har yaushe za mu ci gaba da rasa rayuka kafin a ɗauki mataki na gaskiya?”

NARD ta yaba da jaruntakar waɗanda suka zaɓi ci gaba da zama a Najeriya duk da dusashewar kwakwalwa da ke faruwa, tana kiran su da “’yan ƙasa nagari da jarumai” waɗanda suka cancanci kariya da adalci a biyan haƙƙinsu. Don rage nauyin aiki, ƙungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Lafiya, da ta aiwatar da tsarin maye gurbin likita ɗaya da likita ɗaya (one-to-one replacement policy).

Haka kuma ƙungiyar ta roƙi gwamnati da ta kafa ƙa’idoji masu ƙarfi da za su takaita yawan awannin kiran gaggawa domin kare rayuwar likitoci da marasa lafiya.

“Yayin da Najeriya ke bikin cikar shekaru 65 da samun ‘yancin kai, lokaci ya yi da za a yi tunani ba kawai kan ci gabanmu ba, har ma kan sadaukarwar likitocin gida waɗanda ke riƙe tsarin kiwon lafiya a ƙarƙashin matsanancin yanayi. Ba za mu ci gaba da rasa mambobinmu saboda mutuwar da za a iya kaucewa ba , ba yanzu ba, kuma ba a nan gaba ba,” in ji NARD.


Post a Comment

Previous Post Next Post