Shugaban Kasa Ya Yi Bikin Ranar Yancin Kai a Waje da Abuja

 Karon Farko Tun Bayan Ƙaurar da Fadar Mulki Daga Legas a 1991.

Tunubu

A karon farko tun bayan da aka kaura da fadar mulkin Najeriya daga Legas zuwa Abuja, shugaban ƙasa ya gudanar da bikin ranar samun ‘yancin kai a wajen babban birnin tarayya. Wannan ya kasance wani muhimmin sauyi daga al’adar da aka saba tsawon shekaru inda ake gudanar da bukukuwan a Abuja kawai.

Tun a shekarar 1991 ne aka sauya fadar mulkin ƙasar daga Legas zuwa Abuja, a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Wannan mataki na yanzu ya jawo cece-kuce da kuma jin daɗi daga ‘yan Najeriya da dama, wasu na ganin yana nuni da yunƙurin kawo sabbin dabaru da haɗin kai a cikin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post