Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, ya bayyana godiya ga mambobin majalisar zartaswarsa bisa ayyukan da suka yi da gudummawar da suka bayar wajen cigaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Fubara ya bayyana wannan godiya ne a ranar Laraba, yayin zaman bankwana da aka shirya domin girmama mambobin Majalisar zartaswa a Fadar Gwamnati da ke Port Harcourt, a matsayin wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai.Yayin da yake jaddada muhimmancin ranar ‘yancin kai, gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su haɗa kai da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu wajen gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro, da wadata tare da haskaka makoma ga kowa da kowa.
Haka kuma, ya sake tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da yi wa Jihar Rivers hidima da sabon ƙwazo, tare da gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke ba shi, sannan ya yi wa dukkan ‘yan Najeriya fatan alheri a bikin ranar ‘yancin kai.
A halin da ake ciki, gwamnan ya sallami dukkan kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da hukuncin kotun koli ya shafa daga mukamansu nan take.