Majalisar Jihar Kano Ta Dakatar Da Malami Daga Tattauna Batun Da Ake Zarginsa Da Shi Zargi

 Har Sai An Kammala Bincike, An Haramta Masa Tattaunawa Kan Lamarin.

Lawal Triumph

Sakataren Majalisar, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa Majalisar ta yanke hukuncin dakatar da malamin daga tattauna batun da ake zarginsa da shi, har sai an kammala bincike. Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin da suka janyo cece-kuce a tsakanin jama’a.

Ya ƙara da cewa, malamin zai sami damar kare kansa ta hanyar gabatar da bahasi a gaban Majalisar, sannan daga nan ne za a yanke hukuncin karshe. Wannan dakatarwa ta janyo ra’ayoyi masu tarin yawa, wasu na ganin mataki ne na tabbatar da gaskiya, yayin da wasu ke kallonsa a matsayin wata hanyar tauye ‘yanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post