Shugaba Tinubu Ya Yi Kira Ga Matasan Nijeriya Da Su Yi Mafarkin Zama Manyan Gobe

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci matasan Najeriya da su yi manyan mafarkai, su ƙirƙira sabbin abubuwa, kuma su yi fice a fannoni daban-daban kamar kimiyya, fasaha, wasanni da kuma al’adu.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

A cikin jawabin sa na Ranar ‘Yancin Kai, shugaban ƙasar ya bayyana matasa a matsayin babban arzikin ƙasa da kuma makomar Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na da ƙudirin ƙarfafa matasa ta hanyar manufofi da tallafin kuɗi da aka tsara don ba su “fikafikai su tashi sama”.

“Ina da saƙo ga matasanmu. Ku ne makomar ƙasar nan kuma ku ne babban arzikin wannan ƙasa mai albarka,” in ji shugaban ƙasar.  “Dole ne ku ci gaba da yin manyan mafarkai, ku ƙirƙira, ku kuma ci gaba da cin nasarori a fannoni daban-daban na kimiyya, fasaha, wasanni da kuma fannin al’adu da kere-kere".

Post a Comment

Previous Post Next Post