Yansanda A Jihar Zamfara Sun Yi Babban Kamu

 Jami’an ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama wani sanannen ɗan  ta’adda, mai suna Mohammed Ɗanƙani, wanda aka fi sani da ‘Akki’, tare da ƙwato makamai da harsasai a wasu ayyuka daban-daban.

Makamai

Kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim B. Maikaba, ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake yi wa ‘yan jarida bayani a hedikwatar rundunar a Gusau. A cewarsa, an kama wannan wanda ake zargi mai shekaru 57 kuma ɗan yankin Kuraje ta ƙaramar hukumar Bungudu a Funtua, jihar Katsina, sakamakon bayanan da suka nuna cewa yana da hannu  dumu-dumu ga aikata fashi da satar mutane.

“A lokacin bincike, wanda ake zargi ya amsa laifin cewa yana cikin rukunin da ke ta addabar Tsafe, Yandato, da Yanwarin Daji. Ya kuma amsa cewa yana cikin ƙungiyar Kachalla Ɗan Goggo, wacce aka fi sani da yin garkuwa da mutane a yankunan Damɓa, Mareri, da Saminaka na ƙaramar hukumar Gusau,” in ji Maikaba.

A ranar 15 ga Satumba, jami’an sun kama wata mota Toyota Corolla a titin Gummi–Sokoto tare da ƙwato bindigogi AK-47 guda huɗu, harsasai na PKT guda 200, harsasai na AK-47 guda 28, da kuma kwas guda huɗu. An ɓoye makaman a cikin buhun lemu na wani mai suna Nasiru Dawan Jiya, wanda ya amsa cewa yana jigilar su zuwa ga ’yan bindiga a ƙauyen Gurusu. Hakazalika, a ranar 19 ga Satumba, ‘yan sanda sun kama wasu waɗanda ake zargi guda biyu a babbar hanyar Gusau–Sokoto da wasu bindigogi guda 18.

Post a Comment

Previous Post Next Post