Ana ta raɗe-raɗin cewa kocin Manchester United, Ruben Amorim, na iya yin murabus daga matsayinsa sakamakon rashin gamsar da sakamakon ƙungiyar a wasanni na baya-bayan nan. Sai dai kocin ya musanta wannan jita-jita, inda ya bayyana cewa yana da nisa da barin aiki, kuma ya jaddada cewa ya himmantu wajen gyara ƙungiyar.
A wani ɓangaren kuma, Tottenham Hotspur suna nuna ƙwarin gwiwar ɗaukar ɗan wasan baya na Crystal Palace, Marc Guehi. Rahotanni sun ce Spurs sun miƙa tayin kusan fam miliyan 70, amma Crystal Palace ta ƙi karɓa saboda ƙarancin ‘yan baya a ƙungiyar da kuma ƙin rabuwa da ɗan wasan kafin samun madadin.