Wasu Daga Cikin Sunayen Mutanen Da Suka Yi Fafutuka Wajen Samar Wa Kasar Nijeriya Yancin Kai

 Ranar ‘Yancin Kai, rana ce da kowane ɗan Nijeriya ke farin ciki da murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai. Ƙasar wadda ta samu 'yanci daga Ƙasar Ingila, yau ta cika shekara 65 da kafuwa. A yau Laraba wadda ta yi daidai da 01/10/2025, Najeriya na bikin zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai, rana mai cike da tarihi da alfahari ga ‘yan ƙasar.

Tutar Nijeriya

Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a 1 ga Oktoba, 1960, bayan doguwar gwagwarmaya da jagorancin manyan jarumanmu irin su Sir Ahmadu Bello, Nnamdi Azikiwe, Tafawa Balewa, Obafemi Awolowo da sauran su suka yi. Waɗannan shugabanni sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin an kafa ƙasa mai cin gashin kanta wacce ke tafiya da ƙafafunta. Bayan samun ‘yancin kai, Najeriya ta fara tafiya kan tafarkin ci gaba duk da ƙalubale daban-daban, amma burin haɗin kai da zaman lafiya ya kasance ginshiƙi.

Allah Ya ja kwananki uwa Najeriya,  ya kawo zaman lafiya da cigaba mai dorewa, Amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post