An hango Omoyele Sowore yana gudun fanfalaƙi ana tsaka da zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu #freeNnamdiKanuNow.
A yau ne dai al'ummar Igbo suka shirya zanga-zangaar neman a saki jagoran Biafara wato Nnamdi Kanu domin ya shaƙi iskar 'yanci. Amma ga dukkan alamu haƙarsu ba ta cim ma ruwa ba, domin an hango shugaban zanga-zangar wato matashin lauyan nan Omoyele Sowore yana ta sharar gudu kamar wanda zaki ya biyo sa.