Mai tsaron ragar Senegal Cheiki Toure ya baƙuncin lahira.
Ɗan kwallon ƙasar Senegal Cheiki Toure ya rasu ne a hannun masu garkuwa da mutane, waɗanda suka yi masa yaudare shi ta hanyar kiransa domin shiga wata kungiyar ƙwallo da ke a Ghana. Daga nan ne suka yi garkuwa da shi sannan suka nemi da iyalansa su biya kuɗin fansa, wanda suka kasa biya saboda halin babu, wanda hakan ya zamo ajalinsa.