Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta samu kashi 95 cikin 100 na ƙuri’un da za a kaɗa a jihar a zaben 2027.
Gwamnan ya tuna cewa a zaben 2023, jam’iyyar APC ta samu mambobi huɗu ne kacal a majalisar wakilai, amma yanzu jam’iyyar tana da mambobi 14 a majalisar.Uba Sani ya ce yawaitar sauya sheka zuwa APC a jihar ba wai wani abin al’ajabi ba ne, illa sakamakon tsarin mulkinsa na adalci, gaskiya da haɗin kai.
Yayin da yake jawabi ga sabbin ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyun adawa a babban gangamin APC da aka gudanar a Kaduna a ƙarshen mako, Gwamna Sani ya bayyana cewa yanzu APC tana da mambobi 13 daga Kaduna a majalisar wakilai, yayin da PDP ke da uku kacal.
Haka kuma, a majalisar dokokin jihar, APC na da mambobi 26, PDP kuma na da takwas.
Gwamnan ya ce, “A yau a Kaduna babu jam’iyyar adawa. Na taba gaya wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu watanni da suka gabata cewa muna fatan samun kashi 80 cikin 100 na kuri’u, amma yanzu na canza ra’ayi. A zaben 2027, kashi 95 cikin 100 na kuri’un Kaduna za su tafi ga APC,” in ji shi.
Uba Sani ya kuma tabbatar wa sabbin mambobin jam’iyyar cewa APC jam’iyya ce guda ɗaya da ba ta nuna bambanci, yana mai cewa, “Duk wanda ya shiga jam’iyyar yau da kuma wadanda suka kasance tare da mu tun farko, duk suna da dama ɗaya.”
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana APC a matsayin “ƙasar alƙawari” ga ‘yan siyasar Najeriya, yana mai cewa shugabannin jam’iyyar – Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani – sun cancanci wa’adin mulki na biyu saboda nasarorin da suka samu.
Shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, Hon. Tajudeen Abbas, ya ce jam’iyyar APC ta samu rinjaye a siyasar Kaduna fiye da kowace jam’iyya da ta gabata.
“A yau, ko a yankin Zone 1, Zone 2, ko Zone 3, APC ce jam’iyyar da za a fafata da ita. Ba mu taɓa samun ƙarfi irin wannan ba,” in ji Abbas.
A nasa jawabin, Hon. Husseini Jalo wanda ya yi magana a madadin sabbin ‘yan jam’iyyar, ya gode wa Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kyakkyawan shugabanci da suka nuna a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Babban gangamin ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da Shugaban jam’iyyar na ƙasa Farfesa Nentawe Yilwatda, Shugaban Majalisar Wakilai Hon. Tajudeen Abbas, Ministan Muhalli Alhaji Balarabe Abbas Lawal, da Shugaban Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma, Alhaji Lawal Samaila Yakawada, tare da dubban magoya bayan APC.