Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mai Martaba Sarkin Benin, Oba Ewuare II, murnar cika shekara tara da hawa kan karagar kakanninsa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana godiyarsa ga irin rawar da Oba Ewuare II ke takawa wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai, da ɗorewar kyawawan dabi’u a cikin masarautar Benin da ƙasa baki ɗaya.Shugaban ƙasa ya bayyana cewa Oba Ewuare II ya nuna jajircewa wajen yaƙi da matsalolin da ke addabar al’umma, musamman safarar mutane da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, yana mai jaddada cewa irin waɗannan ƙoƙari sun taimaka wajen kare matasa daga faɗawa cikin hatsarin rayuwa.
Tinubu ya kuma yaba da ƙwazon Oba wajen farfaɗo da al’adun gargajiya da kare kayan tarihi na Afirka, tare da himma wajen dawo da kayan tarihin Benin da aka kwashe zuwa ƙasashen Yamma.
Yayin da Oba Ewuare II ke bikin cika shekaru tara a kan gadon sarauta, Shugaban ƙasa ya jinjina masa bisa irin jagoranci da hangen nesa da ya nuna wajen kiyaye gadon al’adun Benin da miƙa su ga sabbin ƙarni.
Tinubu ya roƙi Allah Ya ba Mai Martaba tsawon rai, ƙoshin lafiya, da ƙarin nasarori a kan karagar mulkinsa.