Sheikh Limanci Dan Kwamitin Shura Na Kano Ya Yi Watsi Da Hujjojin Da Malam Lawan Triumph Ya Gabatar

Malam Lawal Triumph

A cikin wata sabuwar cece-kuce da ke tsakanin malamai a jihar Kano, Sheikh Uwais Limanci, wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan ‘yan Kwamitin Shura na Kano, ya yi watsi da hujjojin da Malam Lawan Triumph ya gabatar a cikin wani wa’azi da ya yi kwanan nan.

Sheikh Limanci ya bayyana cewa hujjojin da Triumph ya dogara da su ba su da inganci kuma suna buƙatar ƙarin bayani daga mahangar ilimin addini. Malamin ya ce akwai bukatar a gudanar da zaman muƙabala tsakaninsu domin a fayyace gaskiya cikin lumana da hujja.

A cewarsa, wannan muƙabala za ta bai wa jama’a damar fahimtar abin da ya dace da gaskiya, tare da kawar da ruɗani da ke yawo tsakanin mabiyan malamai daban-daban.

Sheikh Uwais Limanci ya kuma bukaci hukumomin addini da na tsaro a Kano su tabbatar da zaman lafiya a yayin wannan tattaunawa, idan har Malam Lawan Triumph ya amince da gayyatar.

Rahotanni sun nuna cewa, maganganun Triumph sun jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu kan batun cikin zafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post