Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kano ta saki ɗanjarida Ibrahim Ishaq Rano, wanda aka fi sani da Dan'uwa Rano, bayan tsare shi saboda ƙorafin da jami’in gwamnatin jihar ya shigar a kansa.
Ɗanjaridar ya tabbatar wa BBC cewa an sako shi ne bayan Abdullahi Rogo, babban hadimi ga gwamnan Kano, ya janye ƙorafin da ya shigar a yau Lahadi.
Rogo ya shigar da ƙorafin cewa ɗanjaridar ya ɓata masa suna game da yaɗa labarin zargin da hukumomin yaƙi da cin hanci na Najeriya ke yi masa na ɓatan maƙudan kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin Kano.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana kama ɗanjaridar a matsayin “abin da ya saɓa wa doka”. Ta ce salo ne “da ake amfani da ‘yansanda domin murƙushe kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu”.
An saki ɗanjaridar da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau bayan tsare shi a hedikwatar ofishin yanki na Zone 1 da ke ƙwaryar birnin Kano.
