Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, ya sadu da sabbin shugabannin rundunonin sojojin ƙasar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a wani ɓangare na ƙoƙarinsa na ci gaba da inganta tsarin tsaron Najeriya.
Ganawa sirrin ta zo ne bayan naɗin sabbin hafsoshin tsaro da aka bayyana a matsayin mataki na dabarun gwamnati don haɓaka ƙwarewa, inganci, da ƙarfafa guiwar jami’an rundunonin sojojin ƙasa.Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Manjo Janar Waheedi Shaibu; Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas.
Bayanai game da tattaunawar da Shugaba Tinubu ya yi da sabbin shugabannin tsaron ba su fito fili ba har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto.