Wasu Masana Na Ganin Cewa Mariya Mallon (Typhoid Mary) Ce Mace Ta Farko Da Ta Taimaka Wajen Yada Cutar Typhoid

Typhoid Mary shi ne laƙabin da aka ba wa Mariya Mallon a shekarar 1907. An haife ta a Cookstown cikin kasar Ireland. Mallon ta yi hijira zuwa Amurka a kusa da 1884.

Mary Mallon

Masu binciken lafiya a birnin New York na kasar Amurka sun gano cewa Mary Mallon, wata kazamar mace ’yar kasar Ireland mai aikin dafa abinci, tana ɗauke da ƙwayoyin cutar typhoid duk da cewa ba ta jin duk wani alamu na ciwon ba.

Ita ce mutum ta farko a Amurka da aka gano a matsayin mai dauke da kwayar cutar Salmonella typhoid. Cututtukan sun yi sanadin mutuwar mutane uku, wani kiyasi da ba a tabbatar ba sun kai 50. 

Saboda tsoro, an keɓe ta a tsibirin North Brother Island, kuma aka sanya mata suna (Typhoid Mary).

Bayan shekaru uku an saketa tare da sharadin ka da ta sake dafa abinci. Amma ta yi kunnen kashi, ta ci gaba da aikin dafa abinci bayan da ta canza suna, wanda ya haifar da sake bullar cutar a 1915.

An sake kama ta kuma an sake mayar da ita tsibirin North Brother Island, inda ta rayu a keɓe har shekaru 23.

Bayan fama da bugun jini a 1932, Mallon ta mutu da ciwon huhu a ranar 11 ga watan Nuwamba 1938, tana da shekaru 69. 

An kone gawar Mallon, kuma an binne tokar ta a Sashe na 15, Row 19, Grave 55 (S15-R19-G55) a makabartar Saint Raymond a gundumar Bronx ta birnin New York. Mutane tara ne suka halarci jana'izarta.

Wasu majiyoyi sun yi iƙirarin cewa binciken gawarwaki ya sami shaidar kwayoyin cutar typhoid mai rai a cikin jikin Mallon. 

MUHAWARA

Al'amarinta misali ne na tarihi na rikice-rikice tsakanin 'yancin ɗan adam da lafiyar jama'a. Masu suka sun ce an yi mata rashin adalci kuma an kore ta, yayin da wasu masu sukar ta suka nuna laifinta na ki bin shawarar likitoci bayan sakin ta na farko a matsayin hujjar keɓe ta na dogon lokaci.

Sunanta da aka fi sani, "Typhoid Mary," ya shiga harshen Ingilishi a matsayin kalmar duk wanda ke yada cuta ko rashin lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post