Wani jami’in Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ya ji rauni bayan da wani haɗin guiwar jami’an NDLEA da na rundunar Sojojin Najeriya suka gamu da farmaki a garin Ukpuje da ke ƙaramar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo, a ranar Litinin.
Kwamandan NDLEA na jihar Edo, Mista Mitchell Ofoyeju, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce garin Ukpuje na da suna wajen noman da kuma fataucin tabar wiwi. Ya bayyana cewa yayin da jami’an suka shiga yankin don gudanar da samame, wasu manoman tabar wiwi suka yi musu kwanton ɓauna, lamarin da ya jawo musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.A cewar Ofoyeju, “Dayan jami’anmu an ji masa rauni a hannu sakamakon buguwar wani abu mai kaifi. An kai shi asibiti, kuma yanzu yana samun sauƙi sosai.”
Kwamandan ya jinjina cwa jarumtakar jami’ansa da na Sojojin da suka shiga cikin aikin, yana mai cewa manufarsu ita ce tabbatar da daƙile ayyukan miyagun kwayoyi musamman a wuraren da aka fi sanin irin waɗannan laifuka.
Ya ce, “Ko da mun gamu da cikas, mun gode Allah babu rayuka da suka salwanta, kuma tawagar ta kammala aikin cikin nasara.”
Ofoyeju ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da kai farmaki a sassan jihar domin dakile noman da fataucin miyagun kwayoyi. “Ba za mu daina ƙoƙarin ganin an samu al’umma mai tsafta daga miyagun ƙwayoyi ba. Ayyuka irin wannan suna da matuƙar muhimmanci a yaƙi da muggan ƙwayoyi,” in ji shi.
Harin da aka kai a Ukpuje na cikin jerin matakan da NDLEA ke dauka don yaki da fataucin miyagun kwayoyi tare da kare al’umma.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, hukumar ta kai samame a wurare da ake sayar da miyagun ƙwayoyi a jihar, inda ta kama masu sayarwa, ta kuma samu nasarar gurfanar da wasu gurɓatattun ‘yan kasuwar miyagun kwayoyi a gaban kotu, baya ga shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan illar shan kwayoyi.