Wani Sabon Reshen Kungiyar Boko Haram Ya Fara Mamaya A Jihar Nasawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gargadi jama’a kan mamayar da ake zargin wani sabon reshe na ƙungiyar Boko Haram mai suna Wulowulo ya yi a yankin Arewa ta Tsakiya.

A yayin wani taron tattaunawa da jami’an tsaro a Lafia, babban birnin jihar, gwamnan ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki na Arewa ta Tsakiya su haɗa kai don daƙile barazanar da ke kunno kai.

Binciken yanar gizo bai gano wata cikakkiyar hujja game da wannan ƙungiyar Wulowulo ba, face rassa biyu da aka sani a baya na Boko Haram — Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) da Islamic State West Africa Province (ISWAP) — waɗanda suka samo asali daga rikicin shugabanci a cikin ƙungiyar.

Gwamna Sule ya yi gargaɗin cewa ɓullar wannan sabuwar ƙungiya na iya ƙara taɓarɓarewar tsaro a yankin, wanda tuni ke fama da ayyukan kungiyar Lakurawa da ke addabar wasu sassan Jihar Kwara.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gwamna Sule shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya (NCGF).

A cewarsa:

“Kamar yadda kuka sani, wannan sabuwar ƙungiya ta Wulowulo, wacce ta ɓalle daga Boko Haram, tana fara bayyana a yankin Arewa ta Tsakiya.
Ƙungiyar Lakurawa kuwa ta zama babban ƙalubale a Kwara. A baya suna can kusa da jihohin Kebbi da Sokoto, amma yanzu sun bazu zuwa Kwara, wadda ita ma ke cikin Arewa ta Tsakiya.”

Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa don hana wannan sabuwar ƙungiya shiga Jihar Nasarawa, tare da alkawarin ƙara musu kayan aiki da tallafin aiki.

Wannan taro da gargaɗi sun biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Nindama da ke ƙaramar hukumar Kokona, inda suka kashe mutane takwas da safiyar wani lokaci makon da ya gabata.

Gwamna Sule ya ce an kira taron ne bisa rahotannin tsaro da ke nuna cewa miyagu daga wasu sassan ƙasar na ƙoƙarin shiga yankin Arewa ta Tsakiya.

Ya ce:

“Ɗaya daga cikin dalilan da muka gayyace ku shi ne domin rahotannin tsaro sun nuna cewa matsalolin tsaro a wasu yankuna suna kara ta’azzara, kuma wasu daga cikinsu suna kokarin yaɗa kansu zuwa jiharmu. Don haka dole mu ɗauki matakai kafin abin ya same mu.”

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda matsalar garkuwa da mutane ke ƙara yaɗuwa a wasu yankuna, musamman a ƙananan hukumomin Lafia da Karu.

Gwamnan ya amince cewa dabarun da aka yi amfani da su a baya ba su wadatar ba, don haka akwai buƙatar sabon salo.

“Garkuwa da mutane ta ci gaba da zama matsala, musamman a Lafia. Ta fara daga wasu wurare amma yanzu ta fi ƙamari a Lafia da wasu sassan Karu. Wannan ne yasa nake ganin cewa dabarun da muke amfani da su a baya ba su isa ba. Dole mu nemo sabon tsari don magance matsalar,” in ji Gwamna Sule.

Post a Comment

Previous Post Next Post