Malamai da mabiya addinin musulunci a jihohin Arewacin ƙasar Najeriya sun ɗauki tsawon lokaci suna fafutukar ganin an kafa shari’ar musulunci a sassa daban-daban na kasar.
Biyo bayan kiraye-kiraye na mabiya addinin musulunci ya sanya gwamnan jihar Zamfara a wancan lokacin Ahmad Sani Yariman Bakura ya sanar da cewa jihar Zamfara za ta fara aiki da tsari irin na shari’ar addinin musulunci a ranar 27 ga watan Octoba na shekarar 1999.
Jihar Zamfara itace jiha ta farko da ta fara kaddamar da shari’ar musuluncin a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2000, sai jihar Kano dake biye mata baya inda gwamnan jihar na wancan lokaci Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da shari’ar a watan 6 na shekara ta 2000.
Jihar Sokoto da kuma jihar Katsina sun biyewa jihar Kano baya inda suma suka kaddamar da tsarin shari’ar musulunci a karshen shekarar ta 2000.
Jihohin Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi da kuma jihar Yobe suma sun bi sahun sauran jihohin da suka kaddamar da shari’ar tun da farko a shekarar 2001.
Su kuwa jihohin Kaduna, Niger da kuma jihar Gombe sun kaddamar da shari’ar musulunci ne a wasu sassa na jihohinsu da musulmai ke da rinjaye, kasancewar suna da al’umma da dama masu mabam-bamta addini a jihar. Al’ummar musulmi dai sunyi farin ciki matuka da kaddamar da shari’ar a wancan lokaci.
