Aƙalla mutane goma (10) da ake zargin makiyaya ne sun rasa rayukansu a harin ramuwar gayya da aka kai wa wani sansanin Fulani da ke ƙauyen Tilli, a ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi, a ranar Lahadi.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana hakan ga wakilin LEADERSHIP a Birnin Kebbi. Ya ce harin ramuwar gayya ya biyo bayan kisan da wasu ’yan bindiga Lakurawa suka yi wa ɗaya daga cikin ’yan sa-kai a yankin.
Ya ce, kisan ɗan sa-kan an ɗora laifinsa ne kan Fulani da ke zaune a yankin, lamarin da ya haifar da kai musu farmaki, inda aka kashe sama da mutum goma, wasu da dama kuma suka jikkata a sansaninsu.
A cewarsa, “An kai harin ne bisa kuskure, sun yi tunanin Fulani ne suka kashe ɗan sa-kan. Sun afka musu a sansaninsu, suka kashe fiye da mutum goma, wasu kuma sun ji rauni. Har yanzu ana ci gaba da neman waɗanda ba a san halin da suke ciki ba.”
Majiyar ta ƙara da cewa, jagororin ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association na jihar Kebbi da kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma ya yi alƙawarin bincike a kai.