Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaron Cikin Gida, Hon. Garba Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda da masu zanga-zanga sun yi barazanar tarwatsa da kuma rufe ginin Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin zaman sauraron jama’a kan ƙudirin dokar da ke neman kafa Hukumar Tsaron Majalisar (Legislative Security Directorate), domin tsara ƙa’idojin aiki da cancantar jami’an tsaro na Majalisar, ciki har da Sergeant-at-Arms, a ginin Majalisar da ke Abuja a ranar Talata.Ya ce Majalisar tana fama da matsalolin tsaro da dama, ciki har da satar motoci da babura, lalata kayayyaki, yin jabun katin shaida, shiga ginin ba tare da izini ba, da kuma sayar da kaya a cikin harabar Majalisar wanda ke bata mata suna.
A cewarsa, “Idan ba a ɗauki matakan tsaro masu kyau ba, waɗannan matsalolin za su iya durƙusar da ayyukan majalisa gaba ɗaya – ba za a samu wakilci, duba kasafi ko zama ba, wanda hakan zai kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa.”
Ya ƙara da cewa, ƙudirin dokar da ake tattaunawa a kai yana da matuƙar muhimmanci saboda yana neman samar da tsarin tsaro na zamani kamar yadda ake yi a sauran majalisun duniya.
Muhammad ya ce, “Tsaron majalisa na buƙatar tsarin haɗin kai da tsari na musamman domin tabbatar da cewa muhalli ya dace da gudanar da harkokin majalisa yadda ya kamata.”
Ya ƙara da cewa, “Dole ne Majalisa ta kasance a buɗe ga jama’a domin ci gaba da kare ƙimar dimokuraɗiyya, amma hakan yana nufin cewa ba za a iya ɗaukar matakan tsaro masu tsauri ba tare da la’akari da jama’a ba.”
A ƙarshe, ɗan majalisar ya bayyana cewa ƙudirin dokar zai tabbatar da ingantaccen tsarin tsaro da zai kare ‘yan majalisa, ma’aikata, baƙi da kadarorin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, tare da kira ga Majalisun Jihohi su yi koyi da hakan.