Amurka Ta Matsa Lamba Ga Kwamitin Tsaro Ta Goyi Bayan Shirin Gaza Yayin Da Rasha Ta Gabatar Da Nata Kudirin

 Amurka ta nemi Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ta amince da sabon ƙudirin da ta gabatar domin tsagaita wuta da samar da agajin jin ƙai a Gaza, a daidai lokacin da rikici da halin rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin.

Gaza

Ƙudirin Amurka ya ƙunshi buƙatar a samu tsagaita wuta nan take, a saki dukkan fursunonin da Hamas ke riƙe da su, tare da faɗaɗa hanyoyin isar da tallafin jin ƙai ga fararen hula a Gaza. Amurka ta ce manufar ƙudirin ita ce daidaita buƙatar tsaron Isra’ila da kuma gaggawar kare rayukan Palasɗinawa.

Sai dai Rasha ta gabatar da wani kudiri mai karo da na Amurka, tana mai cewa ba a cika buƙatun samar da zaman lafiya na dindindin ba, kuma ba a yi Allah-wadai da hare-haren Isra’ila ba. Kudirin Rasha ya yi kira da a samu tsagaita wuta ta dindindin ba tare da sharadi ba, tare da suka kan takunkumin taimakon jin kai da ake fuskanta a Gaza.

Masu diflomasiyya sun ce ana ci gaba da tattauna wa kan duka kudurorin biyu, yayin da membobin kwamitin ke da sabanin ra’ayi kan muhimman abubuwa. Ana sa ran za a yi ƙuri’a kan kudurorin a kwanaki masu zuwa, yayin da matsin lamba daga ƙasashen duniya ke ƙaruwa ga MDD domin ta ɗauki matakin kawo ƙarshen rikicin.

Post a Comment

Previous Post Next Post