"Ban Ji Dadin Yadda Yanta'adda Ke Amfani Da Bindigar Da Na Kirkiro Ba" In Ji Mikhail Kalashnikov

 Ina alfahari da kirkiro "AK-47" da na yi, amma ina bakin ciki da yadda ‘yan ta’adda ke amfani da ita. "In ji Mikhail Kalashnikov.

Mikhail Kalashnikov

Mikhail Kalashnikov, wanda ya kirkiri fitacciyar bindigar AK-47, an san shi da bayyana alfahari ga hazakarsa, da kuma tsananin nadama kan yadda makamin ke yaduwa wajen rikici da kuma shiga hannun ‘yan ta’adda.

A cikin wasiƙar da ya rubuta jim kaɗan kafin mutuwarsa a cikin 2013, yana alfahari da ƙirƙirar da ya yi don yin hidima a cikin tsaron ƙasarsa, amma ya damu sosai da "asarar" da bindigar ta haifar a duniya. 

"Ina ci gaba da samun irin wannan tambayar da ban gama warware wa ba: idan bindigata ta hana mutane rayuwa wannnan na nufin cewa ni, Mikhail Kalashnikov ... ni ke da alhakin mutuwar mutane?.

Post a Comment

Previous Post Next Post