Yansandan Nijeriya Sun Chafke Mutum Uku Da Ake Zargi Da Satar Yara A Garin Zariya Da Ke Jihar Kaduna

 Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta kama mutum uku da zargin satar yara tare da ceto wasu yaran 17 a garin Zariya.

Yansandan Nijeriya

Kakakin rundunar SP Mansir Hassan ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an kama mutanen ne bayan tattara bayanan sirri kan wasu yara da aka gani a ƙarƙashin Gadar Danmagaji.

Ya ce jami'an rundunar da suka far wa wurin sun gano yara masu shekaru daban-daban da ake shirin safarar su zuwa Abuja babban birnin Najeriya da wasu yankunan ƙasar.

Rundunar ta ce mutanen da take zargi sun fito ne daga jihohin Katsina da Kano, kuma a cewarta sun amsa laifukan lalubo yaran daga sassa daban-daban da zimmar kai su Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post