Hukumar NPFL mai kula da gasar ƙwallon ƙafa ta firimiyar Najeriya ta ci tarar ƙungiyar Katsina United naira miliyan tara sakamakon hatsaniyar da magoya bayanta suka tayar ranar Asabar.
Wata sanarwa da NPFL ta fitar a yau ta ce mahukuntan Katsina United sun gaza "samar da cikakken tsaro abin da ya jawo magoya baya suka shiga cikin fili" a wasansu da Barau FC a garin na Katsina.
Wasu magoya bayan Katsina sun auka cikin filin ne jim kaɗan bayan Barau ta farke ƙwallon da Katsina ta zira mata, kuma wasu suka jefi ɗanwasan Barau FC Nana Abraham tare da ji masa rauni a wuya.
"An ci tarar kulob ɗin naira miliyan ɗaya kan kowane laifi uku da suka haɗa da jefa abubuwa cikin fili, da rashin tsawatar wa magoya, da kuma haddasa hatsaniya yayin wasa," in ji sanarwar.
"Haka kuma, Katsina za ta biya tarar miliyan biyu kan gazawa wajen samar da cikakken tsaro a filin wasa.
"Sannan za ta biya miliyan biyu kan kowane laifi biyu na ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata, da kuma ɓata wa alƙalan wasa da 'yan Barau FC lokaci bayan tashi daga wasan."
Jimilla Katsina United za ta biya tarar naira miliyan tara kenan, sannan kuma Katsina za ta buga sauran wasanninta na gida a kakar wasa ta bana a garin Jos na jihar Filato.
Hukumar NPFL ta bai wa ƙungiyar awa 48 na ɗaukaka ƙarar hukuncin idan bai yi mata daɗi ba.
