Jihohin Najeriya Da Gwamnatin Birtaniya Ta Yi Gargaɗi A Kaura Ce Wa Saboda Matsalar Tsaro

Gwamnatin Birtaniya ta shawarci yan kasarta su ƙauracewa yin balaguro a wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ta'addanci da satar mutane.

Sanarwar da Gwamnatin Birtaniya ta fitar a shafinta na intanet a ranar Lahadi ta ce matsalar tsaro na ci gaba da ƙaruwa a Najeriya, kuma satar mutane da aikata laifuka da rikicin ƙabilanci sun shafi dukkanin sassan ƙasar.

Wannan na zuwa yayin da Gwamnatin ta ce alkalumman da ta tattara sun nuna ana samun nasarar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi sassan kasar da sama da kashi 80 cikin dari.

Gwamnatin Najeriya ta ce alkalummanta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren da ake kai wa da satar jama'a. "Yanzu ba a satar mutane kamar a baya da ake satar mutum sama da 200 lokaci guda," kamar yadda Abdul'aziz Abdul'aziz ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya ya shaida wa BBC.

Sai dai gwamnatin Birtaniya ta shawarci yan ƙasarta da su yi taka-tsantsan wajen tunanin yin balaguro zuwa sassan Najeriya.

Jihohi 6 masu hatsarin Boko Haram

Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargaɗin a ƙauracewa a yankin arewaci saboda hatsarin hare-haren ƴan Boko Haram da Iswap sun hada da:

  • Borno
  • Yobe
  • Katsina
  • Zamfara
  • Adamawa
  • Gombe

Jihohin da za a yi takatsantsan

Haka kuma, ta bayar da shawarar dakatar da duk wani balaguron wasu jihohin da ke fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan ƴan bindiga.

  • Bauchi
  • Kaduna
  • Kano
  • Kebbi
  • Jigawa
  • Sokoto
  • Neja
  • Kogi
  • Plateau
  • Taraba
  • Abuja (gefen babban birnin tarayya) sai idan ya zama dole.

An shawarci yan Birtaniya su taƙaita yawo a Abuja babban birnin Najeriya inda ta gwamnatin ta ce ana iya samun zanga-zanga da kuma hatsaniya da za ta iya haddasa tashin hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post