Sakamakon yanayin tsaro da ake ciki a Zirin Gaza, yanbindigar da ke yankin yanzu ba wasu shahararru ba ne, ƙananan ƙungiyoyi ne na dangi-dangi da ke adawa da Hamas.
Waɗannan ƙananan ƙungiyoyi sun ɓulla ne saboda rarrabuwar kai da aka samu sakamakon yaƙin Isra'ila da Hamas, wanda ya sa ta rasa iko da zirin.Ƙungiyoyin kan yi iko da abubuwa da yankuna daban-daban, inda suke biyayya ga dangi da 'yan'uwansu.
Amma me muka sani game da waɗannan ƙungiyoyi?
Ƙungiyar dangin Daghmash na ɗaya daga cikin mafiya girma tsakanin zuri'ar Falasɗinawa a Zirin Gaza, inda aka yi ƙiyasin suna da mayaƙa 3,000 a Gaza, da kuma 1,500 a wajensa.
Ta fi ƙarfi a unguwannin Sabra da Tel al-Hawa da ke Birnin Gaza. A cewar jagoran zuri'ar mai suna Salah Daghmash lokacin da yake hira da 'yanjarida a 2007, mambobinta na bin jam'iyyar siyasa daban-daban, kamar Hamas da Fatah, da Popular Front for the Liberation of Palestine.
Mambobin ƙungiyar sun sha gwabzawa da Hamas, musamman bayan Hamas ta kama iko da Gaza a 2007.
Gwabzawar ta fi faruwa a unguwannin Sabra da Tel al-Hawa bayan mambobinta sun ƙi amincewa su miƙa makamansu.