Malaman Musulunci Masu Yawan Mabiya A Shafukan Sada Zumunta A Najeriya

Zamani da kuma fasahar sadarwa sun sa wasu malaman Musulunci a arewacin Najeriya samun ɗaukaka da yawan mabiya a kafafen sada zumunta ko kuma soshiyal midiya.

Hakan kuma ana ganin ba zai rasa nasaba da irin yadda malaman suka karɓi shafukan na soshiyal midiya wajen yin wa'azi da tunatarwa ba.

Hakan ne ya sa aka yi duba da nazari kan shafuka uku - Facebook, Instagram da Youtube na kowane daga cikin malaman guda biyar, inda kuma daga nan muka tattara alƙaluman namu.

Kasancewar Facebook kafar da ta fi tara ƴan Najeriya da ma Afirka, mun ɗauki Facebook a matsayin mizanin farko wajen tantance wanda ya fi yawan mabiya.

Farfesa Sheikh Ali Isa Pantami ya kasance tsohon ministan sadarwa na Najeriya a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Duba ga shafinsa na Facebook, Sheikh Pantami wanda malamin addinin Musulunci ne da ke gudanar da wa'azozinsa a masallacin Annur da ke unguwar Wuse a birnin Abuja, yana da mabiya a shafinsa da suka kai Miliyan biyu.

A shafin Instagram kuma, shehin malamin yana da masu bibiyarsa 858,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post