An cimma tarihi a ƙasar Ostiraliya bayan an rattaba hannu kan yarjejeniyar farko tsakanin gwamnati da mutanen asali na ƙasar (Aboriginal people) a jihar Victoria.
Yarjejeniyar, wacce aka kammala a ranar Alhamis, tana nufin samar da tsarin adalci da daidaito ga mutanen asali waɗanda suka daɗe suna neman ‘yancinsu da ingantaccen wakilci a tsarin gwamnati.
A cewar gwamnatin jihar, wannan yarjejeniya za ta buɗe sabon babi na haɗin kai da sulhu, ta hanyar tabbatar da cewa muryar mutanen asali tana da muhimmanci wajen yanke shawarar da ta shafi ƙasarsu da al’adunsu.
Gwamnan Victoria, Jacinta Allan, ta ce wannan mataki “tarihi ne mai cike da girma,” domin ya nuna cewa Ostiraliya ta fara ɗaukar matakan da suka dace wajen gyara rashin adalcin da aka yi a baya.
Wani jagoran mutanen asali, Marcus Stewart, ya bayyana cewa yarjejeniyar ta nuna cewa an fara samun “gaskiya da adalci” bayan shekaru da dama na gwagwarmaya da ƙin amincewa da hakkokinsu.
Ana sa ran sauran jihohin Ostiraliya za su bi sahun Victoria wajen ƙulla irin wannan yarjejeniya a nan gaba domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da mutanen asali.