Bindigar AK-47 Ta Cika Shekara 78 Da Kirkirowa

 Yau Shekaru 78 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin da ake amfani da su domin kai hari. An haɓaka kirar ta a cikin Tarayyar Soviet ta hannun mai zanen ƙananan makamai na Rasha Mikhail Kalashnikov, shi ne asalin wanda ya kirkiro da bindigar nau'in Kalashnikov (Ko "AK"). Bayan fiye da shekaru saba'in, samfurin AK-47 da nau'ikanta su ka kasance mafi shahara da kuma amfani a duniya.

AK-47

Mikhail Kalashnikov dan kasar Rasha ne kuma shi ne ya ƙirƙiro makamin da ke dauke da sunanshi a tsakiyar a ƙarni na 20.

An haifeshi a ranar 10 ga watan Nuwamba 1919, Kalashnikov ya kasance injiniyan motar yaki a cikin sojojin dake  yaƙin a lokacin yaƙin duniya na biyu. Kuma yaji rauni a lokacin da jamusawa a USSR su ka mamaye su a cikin shekarar 1941.

Mikhail Kalashnikov shi ne mutumin da ya kirkiri shahararriyar bindiga da ake kira AK – 47, ya ƙirƙiri bindigar don sojoji ko wasu dakarun da za su yi amfani da ita don kariya, kuma bai taɓa zaton cewa masu aikata laifi zasuyi amfani da ita ba. 

A Yau wannan bindiga ita ce bindiga da aka fi amfani da ita a duniya. Mikhail ya fara kirkirar bindigar ne a shekarar 1945, an bai wa sojan damar gwajin bindigar a shekarar 1946, kuma an tabbatar da ita kuma an kammala ta a hukumance 1947.

Mikhail Kalashnikov ya mutu a 2013, ya mutu a matsayin babban jarumi a Rasha, amma kafin mutuwarsa, ya rubuta cewa yayi nadama kirkirar wannan makami mai kisa, a cikin wata wasika da aka aike wa shugaban Cocin Orthodox na Rasha a shekarar 2012, a cewar wasikar ya na ta mamakin wai shin shi ne dalilin kashe mutane miliyoyi da akayi da makamin da ya ƙirƙira?. A cikin wasikar tasa, ya ce wannan tambayar guda daya ita ce ke haifar da tsananin ciwo a zuciyarsa. 

Bai kamata a zargi Mikhail ba, saboda kawai ya kirkiro makamin ne a matsayin wani bangare na aikin injiniyancin sa. Amma neman iko da mutane, ya sa mutane suke yin amfani da makamin don kashe miliyoyin mutane don son zuciya da son kai.

Yanzu haka ana samun wannan bindiga a duk duniya, gami da fararen hula Amurkawa masu siye, waɗanda a cikin 2012 suka sayi AK-47 da yawa fiye da yawan da ‘yan sanda da sojojin Rasha ke dasu.

A wani lokaci da yake bayani Mikhail ya bayyana cewar ya kirkiro bindigar AK47 ne domin kariyar Iyakokin kasar sa wato Rasha, sai dai ba laifinsa ba ne, don anyi amfani da ita wajen aikata wasu laifuffuka, wannan a cewar sa, aikin ‘yan Siyasa ne kawai, ya kuma fadi wannan kalamin ne a lokacin da ake bukin karrama shi bisa cika shekaru 90 da Haihuwa a Kremlin.

Ma’anar AK47 dai ita ce, AK na nufin “Kalashnikov's Automatic" sai Lambar 47 da aka samo daga shekarar da aka kera ta 1947.

Akalla dai an nuna cewar an sayar da bindigar AK47 fiye da Miliyan 100 a fadin Duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post