Gwamnatin Amurka ta yi barazanar ƙaƙaba wa wasu gwamnonin arewacin Najeriya, alƙalai, sarakunan gargajiya da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, takunkumi bisa zargin tallafa wa dokokin ɓatanci da kuma nuna halin ko-in-kula ga rikice-rikicen addinai.
ƙudirin doka da ke gaban majalisar dokokin Amurka (Congress) na neman hukunta jami’an Najeriya da ake zargin suna “tallata, aiwatarwa ko ci gaba da riƙe dokokin ɓatanci,” ko kuma “nuna sassauci ga tashin hankali da ake yin amfani da hujjar addini wajen aikata shi.”
Idan aka amince da ƙudirin, sakataren harkokin wajen Amurka zai gabatar da rahoto cikin kwanaki 90, wanda zai lissafa jami’an da za su iya fuskantar haramcin biza, kulle kadarori da takunkumin kudi bisa umarnin shugaban kasa mai lamba 13818, wanda yake ƙarƙashin tsarin Global Magnitsky Human Rights Accountability.
ƙudirin dokar ya kuma haɗa da “alƙalai, majistare, jami’an gidan yari, ko wasu hukumomin shari’a da tsaro” da suka aiwatar da dokokin ɓatanci, ciki har da gurfanarwa, yanke hukunci, da tsare mutane bisa waɗannan dokoki.
An bayyana cewa rahoton da za a gabatar zai shafi shekaru goma da suka gabata kafin dokar ta fara aiki, sannan za a rika sabunta shi duk shekara, don tabbatar da cewa ana duba tsofaffin da sabbin laifuffuka.
Ƙudirin ya ambaci jihohi 12 na arewacin Najeriya — Zamfara, Kano, Sokoto, Katsina, Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi, Yobe, Kaduna, Niger da Gombe — inda aka faɗaɗa aiwatar da dokokin Shari’a tun daga shekarar 1999 har ta shafi manyan laifuka da dokokin tarbiyya.
Ƙudirin ya bayyana dokokin ɓatanci na Shari’a a matsayin masu nuna wariya musamman ga Kiristoci da ƙananan ƙungiyoyin addinai, tare da zargin wasu shugabannin siyasa da na addini na arewa da “ƙarfafa al’adar rashin hukunta masu laifi” da ke haifar da ɗaukar doka a hannu da rashin jituwa tsakanin mabambantan addinai.