Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Joan Laporta, ya bayyana cewa komawar Lionel Messi kulob ɗin ba abu ne mai yuwuwa ba a halin yanzu, yana mai cewa irin wannan magana “ba gaskiya ba ne.”
Yayin wata hira da kafafen yaɗa labaran Catalonia a ranar Litinin, Laporta ya ce duk da cewa Messi ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan da suka fi tarihi a Barcelona, babu wani shiri ko yiwuwar dawowarsa a yanzu.
“Messi yana cikin tarihinmu, kuma koyaushe za a girmama shi a nan Barcelona,” in ji Laporta. “Amma dawowarsa yanzu ba ta yiwuwa. Muna mai da hankali ne kan gina makoma tare da matasan da muke da su da kuma ƙarfafa ƙungiyar.”
Maganganun Laporta sun fito ne bayan jita-jita da dama da ke cewa kulob ɗin na iya dawo da Messi domin buɗe sabon filin wasa na Camp Nou a shekara mai zuwa. Sai dai ya bayyana cewa, duk da yana son Messi ya kasance cikin bikin buɗe filin, ba zai kasance a matsayin ɗan wasa ba.
Messi ya bar Barcelona a shekarar 2021 saboda matsalar kuɗi da ta hana kulob ɗin sabunta kwantiraginsa bisa ƙa’idar Financial Fair Play ta La Liga. A halin yanzu yana taka leda ne a ƙungiyar Inter Miami da ke Amurka.
Laporta ya ƙara da cewa ƙofar Barcelona za ta kasance a buɗe ga Messi a matsayin jakada ko mutum mai girmamawa a nan gaba, amma dawowarsa don taka leda “ba a cikin shirinmu take ba.”